Rahoton wanda manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da ayyukan kiyaye hadurra a kan tituna Jean Todt ya gabatar, ya kuma bayyana cewa daga shekarar 2011 zuwa wannan lokaci, kimanin mutane 1,500 ne suke mutuwa sanadiyar hadurran mota sama da 16,000 a kowa ce shekara a kasar ta Kamaru.
A don haka jami'in ya ce, MDD ta fatan mahukuntan Kamarun za su dauki managartan matakan da za su kai ga dakile kaso 50 cikin 100 na hadrurran dake faruwa a titunan kasar, kamar yadda ke kunshe cikin matakan rage aukuwar hadurran mota da MDD ta tsara. Ya kuma bayyana kudurin MDDr na taimakawa kokarin kasar ta Kamaru na rage aukuwar hadurra a kan titunan kasar. (Ibrahim)