in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Dakarun Boko Haram sun kai hari ga wani kauye
2018-08-21 10:11:51 cri
Dakarun Boko Haram sun cunna wuta ga gidaye 40 a wani hari na ramuwar gayya da suka kai kauyen Mailari na yankin Guzamala dake jihar Borno ta kasar Najeriya, kamar yadda 'yan sandan kasar suka bayyana a Litinin da ta gabata.

'Yan ta'addan sun kaddamar da harin ne kimanin karfe 8 a daren ranar Lahadi, in ji Demien Chukwu, shugaban hukumar 'yan sandan jihar Borno, wanda ya bayyana haka ga manema labaru a birnin Maiduguri, hedkwatar jihar.

A cewar Chukwu har yanzu 'yan sandan ba su tabbatar da yawan mutanen da suka rasa rayuka sakamakon wannan hari ba, amma mazauna wurin sun ce wasu mutane 19 sun mutu.

Sai dai a cewar jami'in, dakarun sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya ga matakan da hukumar kasar ta dauka na kama wasu daga cikin mambobinsu.

An ce, mutane fiye da 20,000 sun mutu daga shekarar 2009 zuwa yanzu sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kaddamar kan al'ummar kasar Najeriya, musamman ma wadanda ke zaune a arewacin kasar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China