A cewar shugaban, gwamnatin za ta yi kokarin kare jama'a, sai dai yana bukatar dukkan jama'ar kasar da su tsaya kan bakarsu don tinkarar abkuwar harin ta'addanci. Ya ce a ko da yaushe, a kuma ko'ina ne za a iya kai hari.
Ban da haka shugaban ya ce, duk da cewa bai yarda da wasu kudurorin da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tsayar dangane da tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya, da yarjejeniyar da ta shafi batun nukiliya na kasar Iran ba, amma kasashen Faransa da Amurka kawaye ne, kuma za su ci gaba da yaki da ta'addanci kafada da kafada.
Yayin da yake magana kan batutuwan tattalin arziki da gyaran fuska game da tsarin zaman al'umma, wandada ke janyo hankalin jama'ar kasar Faransa, shugaba Macron ya ce, jerin matakan da ya dauka tare da zummar samar da guraben ayyukan yi, da raya tattalin arziki, za su fara haifar da sakamako cikin shekaru daya da rabi zuwa shekaru 2 masu zuwa. Ya ce a shirye yake ya gudanar da gyare-gyare a kasar.(Bello Wang)