in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin jiragen Amurka ya hallaka mayakan al-Shabaab 27 a Somaliya
2018-06-05 09:57:04 cri

Rundunar sojin Amurka ta ce harin da dakarunta na musammam suka kai ta sama, ya hallaka mayakan al-Shabaab 27 a arewacin Somaliya.

Rundunar sojin Amurka dake aiki a Afrika (AFRICOM) ta ce an kai harin na ranar Asabar ne da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, a kudu maso yammacin birnin Bosaso.

Wata sanarwar da AFRICOM din ta fitar, ta ce, babu fararen hula da harin ya rutsa da su.

Harin, shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren da dakarun Amurka ke kaiwa kasar dake yankin kahon Afrika da hadin gwiwar dakarun Tarayyar Afrika.

Ana kai galibin hare-haren ne kan jagororin al-Shabaab da sansanoninsu dake kudancin Somaliya, inda har yanzu kungiyar ke rike da wasu yankuna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China