in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya goyi bayan damkawa gwamnatin Somaliya ayyukan tsaro na AMISOM
2018-06-08 10:53:33 cri

Kwamitin sulhun MDD ya yi maraba da irin cigaban da aka samu game da shirin mayarwa hukumomin tsaron kasar Somaliya ayyukan tawagar kiyaye zaman lafiyar kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya wato (AMISOM).

A cikin wata sanarwar ofishin shugaban kasa, kwamitin MDD ya ce shirin musayar ayyukan yana karkashin wasu ka'idoji ne da kuma lokacin da ake son cimmawa, don haka ya bukaci a aiwatar da yarjejeniyar tsaron kasar ta Somaliya domin a cimma nasarar aiwatar da shirin cikin nasara.

A game da wannan batu, sanarwar ta bukaci gwamnatin tarayyar kasar Somaliya da mambobin majalisar kolin kasar, da su bada fifiko a wannan fannin, wanda ya kunshi samar da tallafi daga gwamnatin tarayyar da kuma goyon baya ga dakarun tsaron shiyyoyin kasar.

Haka zalika, kwamitin MDD ya bukaci kasa da kasa da su tallafawa cigaban wannan shirin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China