Guterres wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakinsa Farhan Haq, ya kuma yi imanin cewa, yarjejeniyar ta cancanci a ci gaba da goyon bayanta, kuma akwai bukatar sassan da yarjejeniyar ta shafa su martaba kunshin dake cikinta.
Jami'in na MDD na wadannan kamalai ne, bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya janye kasarsa daga yarjejeniyar kana jiya Talata ya sake dawo da takunkuman da aka janyewa kasar ta Iran.
Ya ce, ko yaya kasa, gwamnati ta dauki wannan batu, MDD ba ta magana a kan manufofin cikin gidan kowa ce kasa.
A jiya ne dai umarnin da shugaba Trump ya bayar na sake kakabawa kasar ta Iran takunkumi,da kuma dakatar da yarjejeniyar nukiliyar kasar(JCPOA) ya fara aiki, bayan da tun farko ya fice daga yarjejeniyar Iran din da aka cimma da kasashen Turai. (Ibrahim)