Gidan talabijin na Press TV ya ruwaito mataimakin shugaban kasar na cewa, kasashen Turai sun yi alkawarin ne a wani yunkuri na rage asarar da Tehran ka iya yi.
A cewar Es'haq Jahangiri, kawo yanzu, takunkuman na Amurka ba su shafi kasashen Turai a fannin tattalin arziki ba, musammam ma game da saye da cinikayyar man fetur.
Ya ce tasirin takunkumin bai yi muni sosai ba, duk da tafiyar wasu kamfanoni masu zaman kansu, musammam na Turai.
A ranar 6 ga watan Agusta ne Shuagaban Amurka Doonald Trump, ya rattaba hannu kan umarnin sanya zagayen farko na Takunkumi a kan Iran domin dorawa kasar matsin tattalin arziki, wanda a baya aka janye karkashin yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015. (Fa'iza Mustapha)