Jami'in wanda ya sanar da hakan ta kafar talabijin din kasar, ya ce an dauki wannan mataki ne, sakamakon ficewar da kasar Amurka ta yi daga yarjejeniyar nukiliyar kasar da kasashen duniya suka cimma (JCPOA).
A halin da ake ciki kuma, Salehi ya ce, janyewar Amurka daga yarjejeniyar ba ta shafi ayyukan Iran na samun makamashin nukiliya cikin lumana ba, ciki har da hakowa, da yin bincike da rayawa ko gina sabbin tashohin samar da makamashi da wasu ayyukan, kamar samar da magunguna ko gina asibitoci.
Ya ce, ayyukan makamashin nukiliyar kasar na gudana babu wata matsala. (Ibrahim)