Jaridar Daily Independent dake da mazauni a birnin Lagos na kasar, ta wallafa cikin kanun labaranta na jiya cewa, "Buhari na fuskantar matsin lamba don ya janye daga sake tsayawa takara"
Mashawarci shugaban kan kafafen watsa labarai Femi Adeshina, ya yi tir da labarin yana mai bayyana shi a matsayin na bogi.
A cewarsa, Shugaba Buhari ba mutum ne mara tunani ba, domin sai da yi nazari mai zurfi kafin ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara.
Ya kara da cewa, wadanda suke tsoron ba za su kai batansu ba idan ya tsaya takara ne ke kokarin sanyaya masa gwiwa ta kowace fuska, ciki har da labaran jaridu da aka dauki nauyinsu. (Fa'iza Mustapha)