in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fursunoni 400 ne suka tsere daga gidan yari a Libya
2018-09-03 14:08:09 cri
Fursunoni 400 ne suka tsere daga gidan yarin Ain Zara dake Tripoli babban birnin Libya a jiya Lahadi, a yayin da rikici tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye ke kara kamari.

Sanarwar da sashen ayyukan 'yan sanda na ma'aikatar shari'a ta kasar ta fitar, ta ce fursunonin sashe na A na cibiyar gyaran hali ta Ain Zara ne suka yi tawaye, bayan da suka ji karar harbe-harben bindiga a kusa da cibiyar, al'amarin da ya yi sanadin gudun 400 daga cikinsu.

Sanarwar ta ce fursononin sun cire kofofi tare da tilastawa jami'an tsaron cibiyar da su kyale su su fice, don kaucewa asarar rayuka, tana mai cewa yanzu haka ana aikin nemansu.

Tun a ranar Litinin, Ain Zara dake yankin kudancin Tripoli, ke fuskantar rikici tsakanin dakarun gwamnati da wadanda ake kira da brigade ta 7 ta 'yan tawaye daga birnin Tarhuna mai nisan kilomita 80 daga kudu maso gabashin Tripoli.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce, kawo yanzu mutane 41 ne suka mutu sanadiyyar rikicin, yayin da wasu 123 suka jikkata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China