Shirin ya bayyana damuwa game da bude wuta kan yankunan dake da yawan al'umma, wanda ya ce barazana ce ga rayukan fararen hula, ya na mai tunatarwa bangarorin biyu hakkin dake wuyansu na kare fararen hula bisa tanadin dokokin tabbatar da 'yancin bil adama da na jin kai na duniya.
Ya kuma jadadda cewa, ba zai yuwu a cimma muradun siyasa ta hanyar rikici ba, inda ya yi gargadin cewa, karuwar 'yan tawaye da rikice-rikice na iya fadada fito na fito tsakaninsu da sojoji.
Hukumar tsaro a Tripoli, ta ce ana fama da rikici a kudancin birnin tsakanin dakarun gwamnatin kasar da MDD ke marawa baya, da 'yan tawaye, wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar farar hula guda da raunata wasu da dama.
Kawo yanzu ba a san musababbin rikicin da aka yi kwanaki ana yi a kudancin Tripoli ba. (Fa'iza Mustapha)