in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi watsi da zargin da ake mata na yanke hukuncin kisa kan magoya bayan tsohuwar gwamnati 45
2018-08-20 09:23:29 cri
Ma'aikatar shari'ar Libya dake samun goyon bayan MDD ta yi watsi da zarge zargen da wasu 'yan adawa daga kasashen ketare ke yi mata sakamakon hukuncin kisa da wata kotun kasar ta yanke kan magoya bayan tsohuwar gwamnatin kasar Libyan su 45.

A wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar ta fitar tace an yi adalci, da bin nagartattun matakai da kuma gudanar da shari'a a kotun bisa ka'idojin da shari'a ta tanada, musamman yadda aka baiwa wadanda ke kare kansu damar daukar dukkan matakan kariya da ka'iojin shari'a suka yarda da su, kuma hakan ya basu damar kare kansu daga irin tuhumar da ake yi musu.

A ranar Laraba ne dai wata kotun shari'a a kasar Libya ta zartar da hukuncin kisa kan wasu magoya bayan tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi bisa zarginsu da laifin kashe masu zanga zanga a Tripoli babban birnin kasar, a lokacin tashin hankalin da ya barke a shekarar 2011.

Ofishin MDD dake Libya (UNSMIL), a ranar Alhamis ya bayyana damuwa game da hukuncin da kotun ta zartar, inda ta kalubalanci yanke hukuncin kisan da cewa ya saba ka'ida.

A ranar 21 ga watan Augastan shekarar 2011, a lokacin da magoya bayan gwamnatin Gaddafi suka hallaka fararen hula masu yawa dake zanga zanga a kusa da babban titin birnin Tripoli.

Wasu fayafayen bidiyo da suka dinga zagawa sun nuna yadda magoya bayan marigayi Gaddafi suke tilastawa masu zanga zangar gurfana akan kafafunsu kafin daga bisani su suka bindigesu nan take. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China