in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hula 130 ne suka mutu yayin rikice-rikice a Libya tun daga farkon shekarar nan
2018-08-20 10:43:59 cri
Shugabar ofishin bada agajin jin kai na MDD a Libya, Maria Ribiero, ta ce fareren hula 130 ne aka kashe sakamakon rikice-rikicen da aka yi a kasar a bana.

Cikin wata sanarwa da ta fitar domin ranar agajin jin kai ta duniya, Maria Ribiero ta ce, kiddidigar MDD ta nuna cewa, a bana, rikice-rikice a Libya sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 130, yayin da wasu da dama suka jikkata, ciki har da yara.

Ta ce al'ummar Libya na kokarin cimma bukatunsu na yau da kullum, yayin da suke cikin matsanancin yanayin samun ilimi da kiwon lafiya.

Jami'ar ta kuma yi kira da a samar da yanayin aiki mai aminci ga dukkan ma'aikatan bada agaji, ta yadda taimakon ceton rai zai rika kai wa ga mutanen da suke bukata ba tare da jinkiri ba a dukkan sassan kasar Libya.

Har ila yau, ta yi kira ga dukkan bangarorin dake Libya, su yi dukkan mai yiwuwa na kare mutane masu rauni, musammam wadanda ke wuraren dake fama da rikici, tare da tabbatar da agajin jin kai ya isa ga masu bukata.

Rikici a Libya na kara ta'azzara, tun bayan rikicin siyasa da ya barke a kasar a shekarar 2011, wanda ya yi sanadin hambare mulkin Muammar Gaddafi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China