in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta dauki alhakin kaddamar da hari a shingen binciken jami'an tsaron Libya
2018-08-26 16:53:01 cri
Kungiyar dake ikirarin kafa daular Musulunci ta IS ta dauki alhakin kaddamar da harin ranar Alhamis a shingen bincike na jami'an tsaron kasar Libya a yammacin birnin Zliten, wanda ya yi sanadiyyar rayuka da jikkata jami'an tsaron.

Wata sanarwar da kafar yada labarai ta IS wato Amaq ta fitar wadda ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, dakarunsu da dama sun kaddamar da hari kan shingen binciken jami'an tsaro na Wadi K'am dake kan titin Zliten, don kaddamar da hari kan jami'an tsaron gwamnati da suke adawa da manufofinsu. Sun yi fito-na-fito da jami'an tsaron inda suka yi amfani da wasu makamai marasa nauyi da gurneti.

Sanarwar ta ce kimanin jami'an tsaro 17 ne suka mutu da kuma jikkata wasu, inda suka tabbatar da cewa dakarunsu masu jihadi sun koma ba tare da koda kwarzane ba.

Tun da farko wasu mutane 4 dake da nasaba da IS a ranar Alhamis cikin wata mota sun kaddamar da hari kan shingen bincike na jami'an tsaro dake yammacin birnin Zliten, mai tazarar kilomita 160 a gabashin birnin Tripoli, ind suka hallaka jami'an tsaro 7 da jikkata wasu mutum 2, kamar yadda wata majiyar jami'an tsaron cikin gida ta tabbatar.

Harin dai ya zo ne kasa da kwana guda bayan da shugaban IS, Abu Bakr al-Baghdadi, ya bukaci magoya bayansa da su gaggauta komawa Libya don taimakawa masu jihadi a Libya, Syria da Iraki. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China