in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi gargadi game da yanayin tsaro a kasar, bayan wani hari da kungiyar IS ta kai
2018-08-24 09:45:58 cri
Gwamnatin Libya da MDD ke marawa baya, ta yi gargadi game da yanayin tsaro a kasar, jim kadan bayan wani mummunan harin da mayakan IS suka kai kan wani shingen binciken dake yammacin birnin Zliten.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar da ta yi gargadin, ta kuma yi kira ga jama'a su ba jami'an tsaro hadin gwiwa tare da bada rahoton duk wani abu da basu yadda da shi ba ko kuma wanda ya sabawa doka.

Da farko a jiyan ne wasu mayakan IS a cikin mota, suka kai hari kan shingen binciken dake Zliten, mai nisan kilomita 160 da gabashin birnin Tripoli, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 7 da jikkatar wasu 2.

Harin na zuwa ne kasa da kwana 1 bayan shugaban kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi ya fitar da wani sakon murya, inda yake kira ga mabiyansa su je su taimakawa mayakan kungiyar dake Libya da Syria da Iraqi.

Ma'aikatar ta kuma tabbatar da samun tsaro tsakanin biranen Zliten da al-Khoms, yayin da kuma za a sake bude babban titin da ya hada biranen da zarar an dauki matakan da suka dace. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China