in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka su shigo a gina shawarar Ziri daya da hanya daya
2018-09-03 14:02:51 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce kasarsa na goyon bayan kasashen Afirka su shiga a dama da su wajen gina shawarar ziri daya da hanya daya ta yadda sassan biyu za su amfana da sakamakon da zai biyo baya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da yake yiwa taron shugabanni da wakilan 'yan kasuwan Sin da Afirka jawabi.

Ya ce, a shirye kasar Sin take ta karfafa alakarta da kasashen Afirka ta yadda za a gina hanyar ci gaba mai inganci da ta dace da yanayin kasashen, ta yadda kowa ne bangare zai ci moriya.

Jawabin shugaban mai take "aiki tare don samun kyakkyawar makoma" shi ne kuma taron 'yan kasuwar Sin da Afirka karo na shida. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China