in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da shugaba Bashir na kasar Sudan
2018-09-03 09:47:07 cri

A ran 2 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan a nan birnin Beijing. A yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya bayyana cewa, bangaren Sin na goyon bayan hanyar neman ci gaba da kasar Sudan ta zabawa kanta, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da kasar Sudan take yi cikin himma da kwazo. Kasar Sin tana neman hadin kan Sudan, wajen fadada hanyoyin hadin gwiwa, ta yadda za a iya bunkasa hadin gwiwar a zo a gani, a fannonin cinikayya da zuba jari, da kuma aikin gona bisa shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya".

A nasa bangaren, shugaba Omar al-Bashir ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sudan da Sin, ya fadada hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe masu tasowa, da kuma tsakanin kasashen Afirka da Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China