Kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen horas da kwararru fiye da dubu 200 cikin shekaru 3 da suka gabata
A wani taron kara wa juna sani game da taron kolin kungiyar hada kan kasar Sin da kasashen Afirka FOCAC da aka shirya a ranar 1 ga watan Satumba, wasu tsoffin direktoci 3 na sashen kula da harkokin Afirka na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin,sun bayyana manufofin da kasar Sin ta dauka kan kasashen Afirka, da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da kuma yadda ake sharen fagen taron kolin na shekarar 2018. Sun bayyana cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata bayan shekarar 2015, gwamnatin kasar Sin ta samar da kudin tallafin karatu ga dalibai dubu 30 wadanda suka fito daga kasashen Afirka kuma suke karatu a nan kasar Sin, har ma ta taimakawa kasashen Afirka wajen horas da mutanen dake da fasahohin zamani iri- iri fiye da dubu 200.
Sannan kasar Sin tana kuma kokarin taimakawa kasashen Afirka a gwagwarmayar yaki da talauci, kuma sun riga sun fitar da wasu kwararan matakan yaki da talauci. (Sanusi Chen)