in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da wasu shugabannin kasashen Afirka
2018-09-02 17:48:11 cri

 

Yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wasu shugabannin kasashen Afirka a nan birnin Beijing, ciki har da shugaban kasar Equatorial Guinea, da na Namibiya da na Sudan da na Senegal da kuma firaministan kasar Mauritius.

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shugaba Xi ya ce, Sin na maraba da Equatorial Guinea don shiga ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", da nuna goyon-baya ga kamfanonin kasar Sin don su inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a a kasar.

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Namibiya, shugaba Xi ya ce, kasar Sin na fatan kara yin mu'amala da cudanya tsakanin manyan jami'anta da na Namibiya, da kara samun fahimtar juna da goyon-bayan juna a kan wasu muhimman batutuwa da dama.

Har wa yau, yayin da yake ganawa da shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, shugaba Xi ya ce, kasar Sin na nuna cikakken goyon-baya ga kasar Sudan kan kokarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, kuma Sin na fatan kara hadin-gwiwa da Sudan a fannin makamashi da ayyukan gona.

Yayin da yake ganawa da shugaban kasar Senegal, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, inganta hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen raya makomar bil'adama ta bai daya, na da muhimmancin gaske ga samun bunkasuwa da inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.

A wani labari kuma, yayin ganawarsa da firaministan kasar Mauritius, Pravind Jugnauth, shugaba Xi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da nunawa Mauritius goyon-baya ta yadda za ta taka muhimmiyar rawa a batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China