in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi taron addu'o'I ga marigayi Kofi Annan
2018-08-23 10:15:15 cri
A jiya ne babban sakataren MDD Antonio Guterres ya jagoranci bikin aza furanni da bude littafin ta'aziya a hedkwatrar MDD dake birnin New York don nuna alhini ga mutuwar tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan.

Guterres ya shaidawa taron cewa, mun hallara ne don nuna girmamawa ga Kofi Annan, daya daga cikin matune na gari a cikinmu, wanda ya martaba akidun MDD ya kuma fitar da mu kunya har maka kira kanmu abokan aikinsa.

Ya ce, shekarun da Kofi Annan ya yi yana aiki sun kasance abin sha'awa. Ya bullo da sabbin manufofi, ya kawo sabbin mutane cikin iyalan MDD, ya kuma yi bayani game da manufofi da ayyukan MDD, Marigayin ya sake dawo da kimar MDD ciki da wajenta game da ayyukan da suka dace majalisar ta yi da kuma yadda za su amfani al'ummar duniya.

A wani labarin kuma, jama'a daga bangarori daban-daban na rayuwa na tururuwa zuwa cibiyar taro ta kasa da kasa dake birnin Accran kasar Ghana (AICC) don sanya hannu a littafin ta'aziyar da aka bude jiya, domin girmama marigayi tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan.

Marigayin ya mutu ne ranar Asabar din da ta gabata a wani asibiti dake birnin Bern na kasar Switzerland, bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China