Ya ce, bisa jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kasar Sin ta cimma sakamako da dama wajen neman ci gaba, ta kuma tsara tsarin gurguzu na musamman da ya dace da yanayin da take ciki.
Ya kara da cewa, tarihin kasar Tanzania ya yi kama da na kasar Sin, sannan ita ma ta gamu da matsala wajen raya tattalin arzikinta, shi ya sa, fasahohin kasar Sin na raya tattalin arziki, za su iya zama abin koyi ga kasar.
Hassan Abbas Ya kuma kara da cewa, a yayin da kasar Sin take dukufa wajen neman ci gaba, tana kuma ba da taimako ga wasu kasashe domin neman ci gaba tare, yana mai cewa shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta fitar a shekarar 2013, ya kuma ba da tallafi ga kasashen duniya da dama. (Maryam)