in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da Sin ta zuba kan ayyukan gina ababen more rayuwa ya dace da bukatun Afirka, in ji shugaban Botswana
2018-09-01 17:03:50 cri
Shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a kasar Sin, ya bayyana cewa, taimakon da kasar Sin ta ba kasashen Afirka wajen habaka ayyukan ginin ababen more rayuwa, ya dace bukatun kasashen Afirka wajen neman ci gaba, yayin da ya kara inganta mu'amala tsakanin kasashen Afirka. Haka kuma, yana ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka bisa fannoni daban daban.

Shugaba Masisi ya ce, taimakon da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka wajen shimfida layukan dogo da ginin hanyoyi da kuma karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen nahiyar, ya ba da gudummawa matuka wajen raya kasashen, yana mai cewa, kasarsa na maraba da kamfanonin kasar Sin, don su kara zuba jari cikin ayyukan dake tallafawa al'umma.

Wannan shi ne karo na farko da shugaba Masisi ke ziyartar Sin, inda daga ranar 3 zuwa ranar 4 ga wata kuma, zai halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da za a yi a nan birnin Beijing.

Yayin taron tattauna harkokin kasuwanci dake tsakanin kasar Sin da Botswana da aka yi a jiya Jumma'a, Mr. Masisi ya bayyana cewa, rashin bunkasar ababen more rayuwa a kasashen Afirka ne ya hana cinikayya a tsakaninsu, amma goyon bayan da kasar Sin ta ba kasashen kan wannan aiki, ya ba da gudummawa matuka wajen warware matsalar. Haka kuma, ya ce, taron dandalin FOCAC da kuma shirin "Ziri daya da hanya daya", sun samar da kyawawan damammaki ga Sin da Afirka wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Har ila yau, Shugaban na Botswana, ya ce an kafa huldar zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ne bisa fahimtar juna da yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu. Yana mai cewa Kasar Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, sannan tana taimakawa kasashen Afirka ba tare da sanya wasu sharadin siyasa ba, abun da ke nuna cewa, kasar Sin ta na girmama bukatun kasashen Afirka wajen neman ci gaba cikin 'yancin. Ya kuma kara da musanta zargin da ake wa kasar Sin na 'mulkin mallaka a kasashen Afirka" inda ya bayyana shi a matsayin mara tushe, yana mai cewa kasashen Afirka sun san yadda za su zabi abokansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China