Haka kuma, ya ce, shawarar "Ziri daya da hanya daya" na sa ran raya kasashen Asiya, Afirka har ma da kasashen Turai, domin cimma moriyar juna. A halin yanzu, kasar Sin ta himmantu wajen shiga cikin ayyukan gina ababen more rayuwa a kasashen Afirka, musamman ma kan ayyukan shimfida layin dogo da tashar samar da wutar lantarki da dai sauransu, lamarin da ya ce ya tallafawa al'ummomin kasar Ruwanda.
Kana, dangane da zargin da wasu mutane ke yi wa kasar Sin game da harkokinta a kasashen Afirka, Mr. Kagame ya ce, kasashen Afirka sun san abun da suke bukata, ta yadda za su iya samun ci gaba, da kuma yadda za su daidaita huldar dake tsakaninsu da manyan kasashen duniya. A ganinsa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na da muhimmiyar ma'ana ga bangarorin biyu wajen samun ci gaba. (Maryam)