in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban Jami'in JKS ya gana da shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou
2018-09-01 15:35:41 cri
Babban jami'in JKS Wang Huning, ya gana a jiya Juma'a da shugaban Niger Mahamadou Issofou, gabanin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika na bana.

Yayin ganawar, Wang Huning, mamba dindindin na kwamitin harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, ya yi kira ga kasashen Sin da Niger, su hada hannu wajen aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen suka cimma a tsakaninsu, tare da musayar bayanai da fadada dangantakarsu da marawa juna baya kan muhimman batutuwan da suka shafe su.

Da yake bayyana yadda Niger ke yabawa nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin aiwatar da manufarta ta gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da yadda take girmama huldar abota dake tsakaninta da Sin, tare da godewa kasar Sin game da goyon bayan da ta dade tana bayarwa ga ci gaban Niger, shugaba Issoufou ya ce a shirye kasarsa take ta zurfafa tare da karfafa huldar moriyar juna da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China