in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Habasha ya ce an kawo karshen tashin hankali a gabashin Kasar sa
2018-08-12 15:51:23 cri
Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya ce an kawo karshen tashe tashen hankula da suka auku a wasu sassan gabashin Kasar.

Abiy Ahmed ya ce an maido da zaman lafiya a yankin bayan da gwamnatin tarayyar kasar, da hukumomin yankin suka dukufa, wajen daukar matakan wanzar da zaman lafiya.

Firaministan ya kara da cewa, jami'an gwamnatin tarayyar kasar, da na yankin na ci gaba da tattaunawa, domin tabbatar da an dakile duk wani yanayi da ka iya haifar da sabon tashin hankali, bayan da tashin hankalin da ya barke a baya bayan nan, ya haifar da rasa rayukan fararen hula, tare da jikkata wasu da dama.

Garuruwa da dama ne dai tashin hankali ya shafa a jihar Somali cikin makon jiya, biyowa bayan tura dakarun sojin gwamnatin kasar zuwa garin Jijiga fadar mulkin jihar Somali a ranar 4 ga watan Agustar nan.

Rahotanni sun ce an dauki wannan mataki ne, domin cafke wasu manyan jami'an yankin, ciki hadda jagoran jihar Abdi Omar Mohammed. Wannan mataki ne kuma ya tunzura tashin hankalin.

Tura sojojin dai ya alamta irin zaman doya da manja dake wanzuwa tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da kuma gwamnan jihar, bayan da gwamnatin tarayyar ta zargi gwamnatin Abdi Omar Mohammed, da keta hakkokin bil Adama.

An ce yanzu haka, wata tawaga karkashin jagorancin Abdi Omar Mohammed din ta isa birnin Addis Ababa, domin tattaunawa da tsagin gwamnatin tarayyar kasar, don tattauna matakan kawo karshen sa in sa tsakanin bangarorin biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China