in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha: 'Yan tawayen ONLF sun bayyana tsagaita bude wuta
2018-08-13 11:03:23 cri
Kungiyar 'yan tawayen ONLF a Habasha, ta bayyana aniyar dakatar da bude wuta, domin ba da damar komawa teburin shawara da tsagin gwamnatin tarayyar kasar.

Cikin wata sanarwar da ONLF din ta fitar, ta ce hakan wata dama ce da za ta share fagen warware sabanin dake tsakanin mahukuntan kasar da na yankin Somali, wanda ya sha fama da tashe tashen hankula.

Kungiyar ONLF, ta ce tana fata za a kai ga cimma matsaya ta kawar da zaman zulumi, a kuma amince da matakan wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin. ONLF ta ce za ta dakatar da duk wasu matakan soji domin kaiwa ga cimma matsaya da tsagin gwamnatin tarayyar kasar.

A watan Afrilun shekarar 2007, ONLF ta kaddamar da wani mummunan hari kan wani wurin hakar danyen mai dake yankin Somali, lamarin da ya sabbaba kisan mutane 65. Jim kadan da aukuwar hakan, sai mahukuntan kasar suka kadddamar da wasu matakan soja na musamman, da nufin dakile tasirin kungiyar ta ONLF a yankin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China