A wata sanarwar da ta rabawa manema labarai, ma'aikatar tsaron ta ce, za ta dauki dukkan matakan da suka dace wadanda suka yi daidai da dokokin kundin tsarin mulkin kasar domin maido da doka da oda da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaron alumma mazauna yankunan jihar Somaliya.
Sanarwar ta kara da cewa, ma'aikatar tsaron kasar ba za ta zuba ido tana kallon tashin hankali yana kara ta'azzara a kasar ba musamman a birnin Jijiga, babban birnin jahar yankin Somaliya. Za ta tabbatar da daukar kwararan matakan bada kariya da tsaro ga mazauna jahar.
Sai dai sanarwar ba ta ayyana wadanda ke da hannu wajen yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin ba, amma matakin ya biyo bayan kwace ikon da dakarun kasar Habasha suka yi ne na majalisar dokokin shiyyar da kuma gidan talabijin mallakar hukumar gudanarwar jahar Somali. (Ahmad Fagam)