in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha: An cafke mutane 108 bisa zargin ta da husuma
2018-08-03 09:52:42 cri
Jami'an tsaro a yankin yammacin Benishangul Gumuz na kasar Habasha, sun cafke mutane 108, bisa zargin su da hannu a tashin hankalin watan Mayu, wanda ya haddasa rasuwar a kalla mutane 10.

Gidan radion Fana dake yankin, ya rawaito babban jami'in watsa labarai na yankin Shiferaw Chelibo, yana cewa cikin wadanda aka tsare hadda wasu 'yan sanda su 20. Jami'in ya kara da cewa, tuni aka gabatar da mutanen su 108 gaban kuliya domin fara gudanar da shari'a.

Garin Assosa na yankin Benishangul Gumuz da kewayen sa, wurare ne da suka sha fuskantar tashe tashen hankula masu nasaba da kabilanci, musamman tsakanin kabilu mazaunan wurin, da kuma wasu kabilu marasa rinjaye dake yankin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China