in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce jami'an bada agaji 313 aka kashe ko aka raunata a bara
2018-08-15 11:26:51 cri
MDD ta ce jami'an bada agaji 313 ne rikici ya rutsa da su cikin mabambantan hare-hare 158 a fadin kasashe 22 a bara.

Jens Laerke, jami'in ofishin hukumar kula da bada agajin jin kai na MDD ne ya bayyana adadin a jiya Talata, gabanin ranar agajin jin kai ta duniya dake gudana a ranar 19 ga watan Augustan kowacce shekara.

Jami'in ya ce daga wancan adadi, 139 ne aka kashe, adadin da ya karu idan aka kwatanta da 107 na shekarar 2016.

A cewarsa, an kai 2 bisa 3n hare-haren ne a kasashe 5 kadai, da suka hada da Sudan ta Kudu da Syria da Afghanistan da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma Nijeriya.

Michele Zaccheo, jami'i daga ofishin watsa labarai na MDD ya shaidawa taron manema labarai da aka yi jiya a Geneva cewa, ranar bada agaji ta duniya ta bana, na da muhimmanci matuka, la'akari da cewa a bana ake cika shekaru 15 da kai harin Bagdad, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an MDD 22, haka zalika a bana ake cika shekaru 11 da harin birnin Algiers da ya yi sanadin mutuwar ma'aikatan MDD 17. (Fa'iza Mutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China