in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi Allah wadai da harin Boko Haram
2018-08-21 10:55:50 cri
Babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da wani harin da dakarun Boko Haram suka kaddamar kan wani kauye dake jihar Borno dake tarayyar Najeriya a ranar Lahadi, lamarin da ya haddasa asaran rayuka da dama, in ji kakakin babban magatakardan MDD, Stephane Dujarric.

Guterres ya yi kiran da a hanzarta gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta'asa a gaban kotu. Sa'an nan ya mika sakon ta'aziya ga gwamnati da al'ummar Najeriya da ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, tare da fatan wadanda suka jikkata za su samu sauki cikin hanzari. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China