in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin shigi da fici na kasar Sin ya nuna goyon baya na ayyukan more rayuwa a kasashen Afirka
2018-08-31 11:03:40 cri
Mataimakin shugaban bankin shigi da fici na kasar Sin Xie Ping, ya bayyana a birnin Beijing a ranar 30 ga wata cewa, bankin ya nuna goyon baya ga ayyukan dake shafar zamantakewar al'umma da rayuwar jama'a musamman a fannonin gina ayyukan more rayuwa, masana'antu, makamashi da sauransu. Ya zuwa karshen watan Yuni na bana, bankin shigi da fici ya gudanar da ayyukan a kasashen Afirka 45 a fannonin sufuri, samar da wutar lantarki, kera kayayyaki, sadarwa, bada ilmi, kiwon lafiya da sauransu.

Xie Ping ya bayyana cewa, bankin shigi da fici na kasar Sin zai yi kokarin inganta karfin raya tattalin arzikin kasashen Afirka a fannoni daban daban da samun kudi ta fitar da kayayyaki da kuma samun ci gaba da kansu bisa hali da bukatu na kasashen Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China