Shugaba Xi ya nuna cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, na maida hankali kan kara raya makomar bil'adama ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, wanda ke da babbar ma'ana ga bunkasuwar dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare, da ingantuwar hadin-gwiwa tsakanin kasashe maso tasowa.
Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta yabawa Kwadibwa saboda matsayinta kan kasancewar kasar Sin daya tak a duk duniya, kuma tana goyon-bayan Kwadibwa ta samu bunkasuwa ta hanyar da ta dace.
A nasa bangaren kuma, Alassane Ouattara ya ce, kasarsa na matukar goyon-bayan shawarar "ziri daya da hanya daya" da shugaba Xi Jinping ya fitar, kuma tana fatan taimakawa kasashe membobin kungiyar ECOWAS don su shiga cikin ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya".(Murtala Zhang)