in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a shirya wani fim game da annobar Ebola
2018-08-30 19:46:06 cri
Yayin da ake shirin kaddamar da taron koli na dandadin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing na kasar Sin a mako mai zuwa, a jiya Laraba, wasu masu shirya fina-finai na kasar Sin da Ghana sun kulla wata yarjejeniya a birnin Beijing, inda suka sanar da cewa za a shirya wani fim mai taken "Ebola". Wannan shi ne karo na farko da masu sana'ar shirya fim na kasashen Sin da Ghana suka yi hadin gwiwa a wannan fanni. Kana fim na farko dake ba da irin wannan labari da ake shirin dauka tsakanin bangarorin Sin da Afirka.

Wannan fim din da ake shirin tsarawa zai bayyana labarin da ya shafi yadda likitoci Sinawa suka gudanar da aikin jinya a yankunan da aka samu barkewar cutar Ebola dake yammacin Afirka a shekarar 2014. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China