in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Saliyo sun lashi takobin kara zurfafa dangantakar kasashensu
2018-08-31 09:46:39 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya gana a jiya Alhamis da takwaransa na Saliyo, Julius Maada Bio, a nan birnin Beijing, inda shugabannin biyu suka yanke shawarar zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu.

Maada Bio ya zo Beijing ne domin ziyarar aiki da halartar taron koli na dandalin tattaunawar Sin da Afrika, FOCAC.

A cewar Shugaba Xi, tun bayan kullawar dangantakar diflomasiya da ta kai shekaru 47, kasashen Sin da Saliyo suka kasance aminai, wadanda ke tsayawa tare da juna a lokacin farin ciki da akasinsa.

Ya tunantar da cewa, yaki da barkewar cutar Ebola da kasashen biyu suka yi cikin hadin gwiwa, abu ne da dukkan al'ummun duniya suka sani, Haka zalika, ya ce Saliyo na daya daga cikin kasashen da suka marawa Jumhuriyar jama'ar kasar Sin baya a kokarinta na dawo da halaltacciyar kujerarta a MDD.

A nasa bangaren, Shugaba Maada Bio, ya ce kasar Sin ta taimakawa kasarsa a fannonin tattalin arziki da inganta zamantakewa, yana mai jadadda cewa, al'ummar kasar ba za su taba manta cewa kasar Sin ce ta ja gaba wajen ba su taimako a lokacin da suka shiga mawuyacin hali na yaki da Ebola ba.

Har ila yau, ya ce a shirye Saliyo take ta koyi darasin samun ci gaba daga kasar Sin, da inganta huldarsu da kuma shiga a dama da ita cikin shawarar ziri daya da hanya daya, tare da zurfafa hadin gwiwa a bangarori da dama.

Bayan ganawar tasu, shugabannin biyu sun rattaba hannu kan wasu daftarorin hadin gwiwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China