Kwamishinan lafiya na jihar Kabiru Getso, ya shaidawa manema labarai cewa, an samu mutane 400 da suka yi fama da matsananciyar gudawa, inda aka tabbatar da 50 daga cikinsu sun kamu da cutar kwalara a fadin kananan hukumomi 33 na jihar.
Daga cikin mutane 50 da aka tabbatar da sun kamu, guda 28 sun mutu, yana mai cewa gwamnatin jihar ta dauki matakai da dama na takaita yaduwar cutar.
Ya ce matakan sun hada da ci gaba da sanya ido kan yankunan dake fuskantar barazanar barkewar cutar tare da binciko wadanda ke fama da amai da gudawa.
Kwalara matsananciyar cuta ce da alamominta ke farawa da gudawa, wanda kuma kan kai ga asarar rai idan ruwan jikin mutum ya kare.
Ana yawan samun barkewar cutar a Nijeriya saboda rashin kyawun hanyoyin samun tsaftataccen ruwa, musammam a yankunan dake da cunkoson jama'a. (Fa'iza Mustapha)