Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar wadda ta tabbatar da umarnin da aka ba babban Sufeton 'yan sandan kasar, ta ce umarnin ya biyo bayan korafe-korafe da kuma rahotannin ayyukan SARS da ake zargin suna take hakkokin bil adama.
Yemi Osinbajo, ya umarci Babban Sufeton da ya sake fasalin sashen tare da tabbatar da kafa wani sashe na ayyukan sirri, da zai mayar da hankali kacokan wajen karewa da farautar 'yan fashi da makami da sace mutane tare da gurfanar da wadanda aka samu da aikata laifukan.
Sanarwar ta kuma ruwaito mukaddashin shugaban kasan na umartar Babban Sufeton da ya tabbatar da sashen na gudanar da ayyukansa bisa tanadin doka da girmama dokokin hakkin bil adama ta kasa da kasa da kuma hakkokin da doka ta tanadarwa wadanda ake zargi.
Har ila yau, Yemi Osinbajo ya umarci hukumar kare hakkokin bil adama ta kasar da ta kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan ayyukan SARS da suka take doka domin ba al'ummar kasar damar gabatar da korafinsu don share musu hawaye. (Fa'iza Mustapha)