Yayin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon CRI a baya-bayan nan, Hadi Sirika ya ce, Najeriya na maida hankali sosai kan taron kolin FOCAC a wannan karo, abun da a cewarsa, zai kawo karin damammaki wajen karfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya. Ya ce, kamfanonin kasar Sin na ayyukan shimfida layukan dogo da gina filayen jiragen sama a Najeriya, har ma a kwanakin baya, Najeriya da Sin sun rattaba hannu kan wata sabuwar kwangilar gina hanyoyin mota. Sirika na fatan taron kolin na wannan karon, zai kara samar da moriya ga Najeriya da Sin har ma ga Afirka baki daya a fannoni da dama, ciki har da zaman rayuwar al'umma, da al'adu, da kuma siyasa.
Har wa yau, Hadi Sirika ya ce Afirka na da dimbin albarkatu, kana, Sin na da karfi sosai wajen raya tattalin arziki da kimiyya da fasaha, don haka yana fatan ganin kasar Sin ta kara zuba jari a kasarsa Najeriya da ma sauran wasu kasashen Afirka.(Murtala Zhang)