in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Burundi: Taron FOCAC dake tafe wata kyakkyawar dama ce ta karfafa hadin gwiwar Sin da Afirka
2018-02-07 19:01:56 cri

Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi ya bayyana cewa, taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC)wadda kasar Sin za ta karbi bakuncinsa cikin wannan shekara a birnin Beijing, wata kyakkyawar dama ce ta karfafa alakar dake tsakanin sassan biyu.

Shugaban wanda ya bayyana haka a Talatar nan yayin zantawa da kafofin watsa labaran kasar Sin, ya ce ya ji dadin yadda aka gayyaci kasarsa domin ta halarci wannan taro mai muhimmanci.

Nkurunziza ya kara da cewa, tun lokacin da aka kafa dandalin FOCAC, kasar Sin take taimakawa Afirka wajen ganin nahiyar ta ci gaba, kuma Burundi ta amfana matuka daga wannan dandali.

Ya ce taron na FOCAC dake tafe wata kyakkyawar dama ce ga kasashen Sin da Burundi na kara zurfafa dangantakar dake tsakaninsu bisa mutunta juna da cin moriya tare, kana wata dama ce ga sauran kasashen nahiyar Afirka ta fadada alakarsu da kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China