in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yara miliyan 570 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a duniya
2018-08-28 11:07:29 cri
Wani rahoton MDD ya ce yara kusan miliyan 570 ne ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a fadin duniya a makarantu.

Rahoton da majalisar ta wallafa a jiya, wanda shi ne irinsa na farko da ya yi nazari kan tsaftar ruwan sha da na makarantu, da hukumar lafiya ta duniya WHO da asusun kula da kananan yara na majalisar UNICEF suka gudanar, ya yi nuni da cewa, yara miliyan 620 ne ba su da bandakuna masu kyau a makarantu, haka kuma kusan miliyan 900 ba sa iya wanke hannayensu da kyau.

Rahoton ya kara da cewa, kusan rabin makarantun ko kaso 47, ba sa samarwa dalibai sabulun da za su yi amfani da shi.

Masu binciken sun kuma gano cewa, yaran dake makarantun Nursery ko Firamare sun fi rashin ruwa da bandaki mai tsafta, fiye da wadanda ke makarantun Sakandare.

Rahoton ya yi gargadin cewa, wannan zai yi mummunan tasiri ga lokaci mai muhimmanci na rayuwar yaran ta fuskar tunani da basira da balaga, yana mai cewa gudawar da ruwa da bandaki mara tsafta ke haifarwa na sanadin mutuwar yara 'yan kasa da shekaru 5 cikin ko wane minti 2.

Har ila yau, rahoton ya kuma jadadda muhimmancin tsaftar jiki da na makarantu musammam ga yara mata, wadanda ka iya zuwa makaranata tare da kammala karatu idan ana kiyaye tsaftar bandakuna da sauran abubuwa a makarantu.

Daya daga cikin muradun ci gaba masu dorewa na MDD shi ne, samarwa mutane tsaftataccen ruwan sha da tabbatar da tsaftar muhalli kawo shekarar 2030. Wannan na nufin samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli a gidaje da makarantu da asibitoci da wuraren aiki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China