in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: An samu kyautatuwar batun auren yara, sai dai akwai sauran rina a kaba
2018-03-07 16:05:19 cri
Bayanin da asusun yara na MDD (UNICEF) ya samar a jiya Talata ya yi nuni da cewa, an samu kyautatuwar batun auren yara a fadin duniya, inda yawan matan da suke in aure a lokacin da ba su kai shekaru 18 da haihuwa ba ya ragu daga kashi 1/4 yau da shekaru 10 da suka wuce zuwa sama da kashi 1/5.

A cewar asusun, a cikin shekaru 10 da suka wuce, sakamakon ingantattun matakan da wasu kasashe suka dauka, yawan auren yara ya ragu da miliyan 25, musamman ma a yankin kudancin Asiya, inda kason ya ragu daga kashi 49% zuwa 30%. A halin da ake ciki yanzu, an fi fuskantar matsalar ne a sassan Afirka dake kudu da hamadar Sahara, inda ake samun auren yara da kaso 38 bisa 100 na matan sassan.

Asusun ya jaddada cewa, domin cimma burin kawar da auren yara kafin nan da shekarar 2030, ya zama dole a gaggauta aiwatar da ayyukan da abin ya shafa. A halin yanzu, mata miliyan 12 suna aure ne a kowace shekara wadanda shekarunsu ba su kai 18 ba. In dai ba a gyara halin ba, nan da shekarar 2030, za a samu mata miliyan 150 a fadin duniya da za su yi auren kafin shekarunsu su kai 18 da haihuwa.

Asusun ya kiyasta cewa, yanzu haka matan duniya da suka kai miliyan 650 sun yi aure ne lokacin da ba su balaga ba. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China