in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta gano miliyoyin mutane karkashin kangin bauta na zamani da bautar da yara kanana
2017-09-20 10:13:31 cri

Wani rahoton MDD ya gano kimanin mutane miliyan 40 ne a halin yanzu suke rayuwa karkashin wani sabon salo na bautar da dan adam, kuma galibin mutanen da lamarin ya shafa mata ne da kananan yara, kana kimanin yara kanana miliyan 152 ne ake bautar da su, a kalla yaro guda cikin yara 10 a duniya na fama da wannan matsala.

Sabon binciken na hadin gwiwa ne tsakanin hukumar kwadago ta kasa da kasa ILO, da gidauniyar Walk Free Foundation, da hukumar kula da makaurata ta duniya IOM, ya nuna a zahiri yadda ake aiwatar da sabon salon bauta na zamani a duniya.

Babban daraktan ILO, Guy Ryder, ya bayyana cewa, duniya ba za ta samun dauwamamman ci gaban zamani ba, matukar ba'a dauki matakan yaki da wannan muguwar dabi'a ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China