in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tauye rayuwar kananan yara a duniya, inji babban jami'in MDD
2017-11-21 12:47:07 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya tsage gaskiya inda ya bayyana cewa, duniya tana tauye rayuwar kananan yara ta hanyar jefa su cikin mawuyacin hali da kuma matsananciyar rayuwa.

Da yake jawabi a gaban dandazon yara kanana a helkwatar MDD dake birnin New York a bikin ranar yara ta MDD wanda majalisar ta kebe ranar 20 ga watan Nuwambar kowace shekara, Guterres yace, "a yi mini afuwa, dole ne na tsage gaskiya, mu manya muna durkusar da rayuwarku yara".

Yace, "miliyoyin yara mata da maza kamar ku, rayuwarsu tana cikin garari, kuma muna durkusar da rayuwar ku. Yara na tserewa tashin hankali dake haddasa salwantar rayuka. Yara na fama da matsananciyar yunwa, babu magungunan da suke bukata. Sun rabu da iyayensu, ko kuma yin nesa da iyayen nasu, suna yin wata tafiya mai cike da hadari. Sun tarwatse kuma suna rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira wanda yayi nesa daga gidajensu".

"Yara da yawa suna fuskantar muzgunawa a shafukan internet ko kuma a makarantu, ko kuma suna fuskantar nuna wariya saboda addinansu, ko launin fatarsu, ko kabilarsu. Kuma a mafi yawan lokuta, suna fadawa cikin matsala sakamakon tashe tashen hankula ko bautarwa daga hannun manya".

Guterres yace, dukkan wadan nan ba abubuwan da za'a lamince ba ne. Yace duniya ba zata zuba ido tana kallon yadda ake cigaba da musgunawa kananan yara ba.

Kana yayi alkawarin cewa MDD zata cigaba da yin aiki ba tare da kakkautawa ba, domin ganin rayuwar kananan yara ta kyautata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China