in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu na MDD ya amince da wani kudurin kare yara a yayin rikici
2018-07-10 11:16:02 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya amince da wani kuduri dake da nufin kare yara yayin da ake rikici, ta hanyar daukar wasu matakai.

Kudurin mai lamba 2427, wanda ya samu amincewar daukacin mambobin kwamitin 15, ya yi suka kan horar da yara da amfani da su da bangarori masu rikici ke yi, tare kuma da kashewa da cin zarafinsu, da yi musu fyade da sauran cin zarafi ta hanyar lalata da kuma sace su.

Kudurin ya kuma yi tir da hare-hare kan makarantu da asibitoci da hana kai agajin jin kai da bangarori masu rikici ke yi, da take dukkanin dokokin kasa da kasa da suka shafi kare yara a lokacin rikici.

Ya kuma bakuci dukkanin bangarorin dake rikici su kawo karshen wadancan dabi'u tare da daukan matakai na musammam domin kare yara.

Har ila yau, kudurin ya jadadda nauyin dake wuyan dukkan kasashe na kawo karshen cin mutunci tare da gudanar da bincike da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata kisan kiyashi da take hakkokin dan adam da laifukan yaki da sauran laifukan da suka shafi yara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China