in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum guda ya hallaka, kana wasu mutanen 4 sun jikkata a wasu harbe harbe a California
2018-04-04 11:06:57 cri
Hukumomi sun tabbatar da cewa an hallaka mutum guda kana wasu mutanen 4 sun samu raunuka a wasu harbe harbe da aka yi a helkwatar YouTube dake jahar California ta Amurka.

Wani jami'in 'yan sanda Ed Barberini a birnin San Bruno, dake da tazarar kilomita 19 a kudancin tsakiyar birnin San Francisco a yammacin Amurka ya bayyana cewa, ana zargin wata mace ce ta kaddamar da harbe harben, inda daga bisani kuma ta harbe kanta bayan da ta raunata mutane masu yawa a harabar ginin ofishin na YouTube.

An yi harbe harben ne da misalin karfe 12:48 na yammaci, a wajen harabar ofishin na YouTube wanda rukunin gidajen ke dauke da ma'aikata kimaini 1,700.

Jami'an 'yan sanda suna cigaba da bincike domin gano ko akwai wasu maharan a cikin ginin.

Barberini ya bayyana cewa, an garzaya da mutanen 4 da suka jikkata zuwa wani asibiti mafi kusa domin ba su maganin raunukan da suka samu a sanadiyyar harbin bindigar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China