in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu adawa da 'yan kishin farar fata sun yi gangami a Washington
2018-08-13 10:13:56 cri
Dubban masu adawa da 'yan kishin farar fata sun yi gangami a wasu sassa na birnin Washington da yammacin jiya Lahadi, sa'o'i kadan gabanin gangamin da masu kishin fararen fata za su gudanar.

Masu adawar dai sun taru a gandun shakatawa na "Lafayette Park" dake daura da fadar White House, da kuma dandalin "freedom plaza" mai makwaftaka da shi.

Masu adawar dai na bikin cika shekara guda, bayan gangamin masu kishin farar fata da ya gudana a Charlottesville, wanda ya rikide zuwa tashin hankali, har ya kai ga hallaka wata mace mai adawa da taron.

Domin gujewa barkewar rikici, jami'an tsaro a Washington sun kewaye sassan da tarukan ke gudana. An kuma jibge 'yan sanda a kewayen titin Pennsylvania dake daura da fadar White House.

Masu rajin kishin farar fata da ake kira "United the Right 2" a Turance, na cewa burinsu shi ne kare hakkokin fararen fata. To sai dai Amurkawa da dama na kallon su a matsayin masu rura wutar kyamar sauran jinsi, da nuna wariyar launin fata.

Masu adawar sun rika daga alluna masu dauke da bayanai na kyamar wariyar launin fata, da mulkin mulaka'u, suna masu kira da a rungumi aki'dun kaunar juna. A wasu lokunan kuma su kan kaure da sowa, suna rera wakokin dake bayyana manufofin su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China