in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 8 sun mutu, wasu da yawa kuma sun jikkata sanadiyyar harin da aka kai birnin NewYork
2017-11-01 10:59:49 cri

Magajin Garin Birnin New York Bill de Blasio, ya ce mutane 8 sun mutu, yayin da wasu gommai suka raunana, biyo bayan kutsawa hanyar matafiya da kafa da wata babbar mota ta yi a kusa da cibiyar cinikayya ta duniya dake birnin.

Yayin wani taron manema labarai, Magajin garin ya ce bisa bayanan da hukumomi suka tattara, harin na tsoro ne da a kai kan fararen hula da basu ji ba, ba su gani ba.

Shi ma da yake jawabi yayin taron, kwamishinan 'yan sandan birnin James O' Neil, ya ce wanda ake zargi da kai harin mai shekaru 29 ba dan birnin na New York ba ne. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China