in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 sun mutu, wasu da dama sun jikkata a harin da aka kai wani gidan jarida a Amurka
2018-06-29 13:28:45 cri
Mutane 5 sun mutu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, sanadiyyar harbin kan uwa mai dawabi da wani ya yi kan gidan jaridar Gazatte dake birnin Annapolis na jihar Maryland dake gabashin Amurka.

'Yan sanda sun ce an cafke maharbin inda ake masa tambayoyi, sai dai ba su bayyana ko wane ne ba.

Wasu rahotanni da ba a tantance sahihancin sub a na cewa, wanda ake zargin ya bude wuta ne inda ya yi ta harbi.

'Yan sandan sun kara da cewa binciken farko sun nuna cewa maharin na aiki ne bisa radin kansa.

Wani ma'aikacin gidan jaridar Phil Davis, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, maharin ya yi harbin ne ta cikin kofar gilas, kuma mutane da dama ne harbin ya rutsa da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China