in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jamiyyar adawa ta MDC a Zimbabwe ta kalubalanci nasarar da Mnangagwa ya samu
2018-08-11 15:47:28 cri

A Juma'ar da ta gabata jam'iyyar kawancen adawa ta MDC a Zimbabwe ta garzaya kotu inda ta bukaci a soke nasarar da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa ya samu a zaben kasar na ranar 30 ga watan Yuli.

Hukumar zaben kasar ta sanar da cewa, Mnangagwa ya samu kashi 50.8 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Nelson Chamisa, na MDC Alliance, wanda ya yi watsi da sakamakon zaben, inda ya yi zargin an tafka magudi a zaben.

Lauyan dake kare mista Chamisa, Thabani Mpofu ya fadawa 'yan jaridu cewa, "Mun shigar da kara. Muna neman kotu ta gaggauta soke zaben shugaban kasar wanda aka gudanar da shi ba bisa ka'ida ba, ba'a gudanar da zaben bisa kundin tsarin mulkin kasa ba, ba'a gudanar da zaben bisa tanade-tanaden dokokin hukumar zaben kasar ba kuma ba'a gudanar da zaben bisa gaskiya da adalci da sahihanci ba".

Sun bukaci kotun ta dakatar da shirin rantsar da Mnangagwa wanda aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China