in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke daya daga jagororin 'yan adawa a Zimbabwe
2018-08-08 19:25:36 cri
Jami'an tsaro a Zimbabwe sun cafke Tendai Biti, daya daga cikin jiga jigan jami'iyyar adawa ta MDC a kan iyakar kasar da Zambia. Rahotanni sun bayyana cewa, an cafke Mr. Biti ne a Larabar nan, lokacin da yake kokarin tserewa Zambia domin neman mafakar siyasa.

Lauyansa Nqobizitha Mlilo ya tabbatar da kame Biti, inda ya ce jami'an tsaron sun damke shi ne a yankin Chirundu, dake kan iyakar Zimbabwe da Zambia.

Kame Biti dai ya biyo bayan sanarwar da jami'an tsaro suka fitar a Litinin din da ta gabata, inda suka anya shi, da sauran wasu kusoshin jami'iyyar adawa ta MDC su 8 da hannu, cikin tashin hankalin da ya barke, bayan fidda sakamakon zaben shugaban kasa a birnin Harare, fadar mulkin kasar, lamarin da ya sabbaba kisan mutane 6, tare da raunata wasu da dama. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China