Mataimakin kakakin babban sakataren MDD Farhan Haq, ya shaidawa manema labarai cewa, jiya Talata babban sakataren MDDr ya tattauna ta wayar tarho da shugaba Mnangagwa da kuma jagoran jam'iyyar MDC Nelson Chamisa, inda ya bayyana musu karara cewa, yana fatan shugaban na Zimbabwe zai tabbatar da cewa, jami'an tsaro sun yi taka tsan-tsan. Ya kuma karfafawa bangaren adawa gwiwar da su gabatar da kokensu na siyasa ta hanyar da doka ta shata.
Babban sakataren MDDr ya kara da cewa, ya kamata duk wani hukunci da kotu ta yanke game da sakamakon zabukan ya kasance mai zaman kansa.(Ibrahim)